Cote d’Ivoire

Kungiyar ECOWAS ko CEDEOA ta kira taro kan kasar Cote d'Ivoire

Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afrika ta Yamma ECOWAS-CEDEOA ta ce zata gudanar da taro a wannan makon kan rikicin siyasar kasar Cote d’Ivoire.A cikin watan sanawar kungiyar ta bayyana gudanar da taron ranakun 23 da 24, inda zata duba yunkurin shiga tsakani kan rikicin.Kasar ta Cote d’Ivoire ta fada cikin rikicin bayan Laurent Gbagbo yaki amincewa da sakamakon zaben da Alassane Ouattara ya lashe.Kungiyar ta ECOWAS-CEDEOA, ta kuma nemi ‘yan siyasar kasar Janhuriyar Benin su amince da sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar, kuma duk mai korafi ya nufi kotu, domin daukan matakan sharia da suka dace. 

AFP/Issouf Sanogo