Masar

An samu fitowar masu zabe raba gardama na Masar

Masu zaben kasar Masar
Masu zaben kasar Masar Reuters

An samu gagarumin fitowar masu zabe, yayin zaben raba gardama bisa sabon kundin tsarin mulkin kasar Masar, wata guda bayan kawo karshen mulkin Hosni Mubarak na shekaru 30.Yau Lahadi ake saran fara samun sakamakon farko na zaben, kuma idan an amince da kundin, za a gudanar da zabuka cikin watanni shida.Yayin zaben wasu sun kai hari kan Mohamed ElBaradei tsohon Shugaban Hukumar kula da Makamashin Nukiya ta MDD, yayin da yake shirin kada kuri’a, a Alkahira babban birnin kasar.ElBaradei yana cikin wadanda suka bayyana sha’awar takarar shugabancin kasar ta Masar.