Ana ci gaba da ruwan watar wargaza karfin dakarun Gaddafi na Libya
Shugaban kasar Libya, Muammar Ghaddafi, ya ce a shirye suke su fafata da dakarun Yammacin Duniya dake kaiwa kasar hari, yayin da aka shiga rana ta hudu na wadannan hare hare, inda ya ke cewa zasu samu nasara.Tashar talabijin din kasar, ta nuna hotan shugaban yana shaidawa magoya bayansa cewa, suna tare da nasara, yayin da akaji fashewar manyan makamai a birnin Tripoli, sakamakon hare haren.Tuni fadar Shugaban kasar Amurka, ta ce shugaba Nicolas Sarkozy na Faransa, da David Cameron PM Britaniya, da kuma Barack Obama, sun amince da rawar da Kungiyar Tsaro ta NATO, zata taka a kasar ta Libya.Fadar tace, bayan tatatunawar da shugabanin uku sukayi ta waya, sun ce an samu nasarar hana dakarun shugaba Ghaddafi kara matsawa Benghazi, da kuma maincewa da rawar da NATO zata taka wajen aiyukan tsaron Libya. A wani labarin hukumomin kasar ta Libya, sun sako 'yan Jaridun Kanfanin Dillancin Labaran Faransa da suka kama ranar juma’a, Dave Clark da Robert Schmidt, tare da wakilin kanfanin Getty, Joe Radle, wadanda yanzu haka ke Rixos hotel a Tripoli.Shugaban kanfanin Dillancin labaran Faransa, Emmanuel Hoog, ya bayyana farin cikinsa da sakin.
Wallafawa ranar: