Italiya

Bakin Haure na kwarara zuwa Italiya daga Arewacin Afrika

Cinkoson bakin haure ya kaure a tsibirin Lampadusa na kasar italiya, inda majalisar Dinkin Duniya ta nemi a dauki matakan gaggawa wajen magance matsalar.Jiragen ruwa guda biyar ne dake dauke da bakin haure 291, suka isa a gabar ruwan tsibirin Lampedusa na kasar Italiya, wanda ke nuna yawan bakin hauren da aka jibge a dan karamin tsibirin na kasar Italiya dake makwabtaka da gabar ruwan kasar Tunisiya da cewa sun haura 6000.Yanzu haka dai lamurra sun tsaya cik da dan tsibirin dake da fadin maraba’ain km 20, inda aka jibge bakin haren sama da 6000 a cibiyar da bata wuce daukar bakin hauren 850 kacal.Ko a jiya Talata Wani jirgin ruwan sojan kasar ta Italiya ya yi safarar bakin haure 700 zuwa tsibirin duk da kiran da hukumar yan gudun hijira ta MDD HCR ta yi na kwashe daukacin bakin hauren dake cibirin cikin gaggawa, zuwa wasu sansanonin na daban.ministan cikin gidan kasar Italiya Roberto Maron ya bayyana samun amincewar wasu yankunan kasar ta Italiya, da cewa zasu karbi kimanin bakin hauren dubu 50 a cikinsu.An dai kiyasta cewa tun farkon wannan shekara kawo yanzu, kimanin bakin haure dubu 15 ne suka kutsa kai a kasar ta italiya, wanda ke nuna cewa ya rubanya sau uku bisa na 2010 da ta gabata.