ECOWAS

Kungiyar Kasashen Afrika ta Yamma na Taro kan kasar Cote d'Ivoire

Reuters/Luc Gnago

Kungiyar Kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS, yau zata gudanar da taron ta a birnin Abuja na Tarayyar Nigeria, wanda ake saran zai maida hanakali kan halin da ake ciki a kasar Cote d’Ivoire mai fama da tashin hankali.Ko a wannan karon taron zai dauki kwararan matakan da zasu kawo karshen rikicin Cote d’IVoire, tambayar kenan da muka yiwa Dr El Harun Muhamed, mai sharhi kan al’amuran yau da kullum.A wani labarin zabebben Shugaban kasar Cote d’Ivoire, Alassane Ouattara, ya zargi dakarun Majalisar Dinkin Duniya, da kin kare faraen hula a cikin kasar, abinda ya haifar da kashe mutane sama da 800 da dakarun Laurent Gbagbo sukayi.Amma kakakin Majalisar Dinkin Duniya a cikin kasar, Hammadoun Toure, ya ce ba aikin su bane yaki da dakarun gwamnatin kasar ta Cote d'Ivoire masu biyayya wa Gbagbo dake ci gaba da karfa karfa kan madafun ikon kasar, bayan zaben da ya fadi.