Mahukuntan Najeriya sun kamkado masu hada bama bamai a garin Jos
Rundunar Sojin dake aikin samar da tsaro a Jihar Plateau dake Tarayyar Najeriya, ta gano masana’antar da ake hada bama bamai a unguwar Millionnaires Quarters dake birnin Jos.Kakakin rundunar Manjor Charles Ekeocha, ya ce jami’ansa ne suka kama wasu matasa biyu, masu suna Dantala Babawo, da Christopher Datung Peter, dauke bam din akan babur, bayan sun musu tambayoyi sai suka kaisu gidan da ake hada bama baman, inda suka samu masana’antar, da kuma litattafai na koyar da yadda ake hada bama baman.Jami’in ya ce, ba suyi nasarar kama mai gidan su ba, mai suna Frank Anyok, wanda yanzu haka suke nema ruwa a jallo.Ko a karshen makon da ya gabata, sai da wani bam ya fashe a garin, inda ya hallaka yara biyu masu dauke da shi.
Wallafawa ranar: