Libya-Masar

Sakataren Tsaron Amurka Gates ya isa Masar kan rikicin Libya

Robert Gates, Sakataren Tsaron Amurka
Robert Gates, Sakataren Tsaron Amurka REUTERS/Jim Young

Sakataren Tsaron kasar Amurka Robert Gates ya fara ziyarar aiki a Alkahira babban birnin kasar Masar, domin tattaunawa kan rikicin kasar Libya.Zai kuma jaddada goyon bayan gwamnatin Amurka bisa shirin mayar da kasar ta Masar kan turbar demokaradiya, bayan boren da ya kawo karshen gwamnatin Hosni Mubarak ta shekaru 30.Rikicin siyasar kasar ta Libya ya rikide zuwa yakin basasa, wanda ya kai Kwamitin Sulhun MDD ya saka takunkumin haramta shawagin jiragen sama a sararin samaniyar kasar ta Libya.Yanzu haka manyan kasashen Yammacin Duniya karkashin Amurka, Birtaniya da Faransa suna aikin tabbatar da kudirin na MDD, tare da ruwan wuta na wargaza karfin sojan dake biyayya wa shugaban na Libya Muammar Gaddafi.Gaddafi ya ci gaba da nuna turjiya, inda ya ce zai samu nasara kan hare haren da ake kai masa, yayin da ya yi jawabi wa al’umar kasar ta kafofin yada labaran kasar.