ECOWAS ta bukaci Majalisar Dunkin Duniya daukar mataki kan Cote d’Ivoire
Kungiyar Kasashen Afrika ta Yamma, ta bukaci Majalisar Dunkin Duniya kan daukar kwararan matakai don magance rikicin siyasar kasar Cote d’Ivoire. Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya bayyana cewa tashin hankali a kasar wata barazana ce ga sha’anin tsaro ga kasashen yammacin Africa.Lokacin da ya ke jawabi bayan bude taron kungiyar da aka gudanar a Abuja, Mista Jonathan yace yana fatar za’a magance rikicin kasar ba tare da amfani da karfin soji ba.Kasar Angola ta bayyana goyon bayanta ga matakin kungiyar tarayyar Africa wadanda suka amince da Alassane Ouattara a mtsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar duk da cewa Laurent Gbagbo ya ki amincewa ya sauka daga shugabancin kasar bayan ya sha kaye a zaben da aka gudanar a watan Nuwamban bara.A yanzu haka dai kimanin mutane 400 ne suka rasa rayukansu, yayin da dubun dubutar ‘yan kasar suka yi gudun hijira daga kasar ta Cote d’Ivoire zuwa wasu kasashe da ke makwabtaka da kasar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Tattaunawa da Buhari Mohammed Bello Jega, directa a cibiyar bincike kan siyasa da ci gaban kasa, a Abuja
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu