Libya

Kasashen Duniya na ci gaba da Rufe Asusun bankunan Gaddafi

Kasar Tunisiya da ke Makwabtaka da kasar Libya ta sanar da rufe asusun shugaban kasar Libya Muammar Gaddafi wanda ya hada da na iyalansa a kasar.A daidai wannan lokacin ne kasar Zambia ta bayyana dakushe dangantakar kasuwanci ta fannin sadarwa da kasar Libya tare da bayyana rufe asusun shugaba gaddafi a bankunan kasar.Wannan dai na zuwa ne bisa wani umurni daga majalisar Dunkin Duniya. 

Shugaban Libya Muammar Gaddafi
Shugaban Libya Muammar Gaddafi REUTERS