Benin-Nigeria

Soglo ya soki Jonathan kan zaben kasar Benin

Tsohon Shugaban kasar Benin Nicéphore Soglo.
Tsohon Shugaban kasar Benin Nicéphore Soglo. AFP

Tsohon Shugaban kasar Jamhuriyar Benin, Nicephore Soglo, ya soki shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan, a ziyarar da ya kai kasar ranar juma’a, inda yayi gargadi kan samun rikicin dake da nasaba da zabe.Soglo yace ba su amince da matsayin shugaba Jonathan ba, a wannan hali da suke ciki, kan abinda tsohon shugaban ya kira magudin zabe da aka tafka, wanda ya baiwa shugaba Boni Yayi nasara.