Nigeria

‘Yan Sandan Nigeria sun sha alwashin samar da tsaro a yankin Niger Delta lokacin zabe

'Yan Sandan Nigeria
'Yan Sandan Nigeria

Rundunar ‘Yan Sandan Nigeria, ta yi alkawarin samar da tsaro a Yankin Niger Delta, domin ganin an gudanar da zabe lafiya ba tare da wata barazana ba.Mataimakin Sufeto Janar na Yan Sanda, mai kula da shiya ta shida, Muhammad Dikko Abubakar ne ya shaidawa sashen hausa na RfiYankin Niger Delta dai ya dade yana fama da rikici musamman barazanar da tsagerun Yankin ke yi. Asali ma a kwanukan da suka gabata kungiyar MEND mai fafutikar ‘yancin Niger Delta ta yi gargadin kai hare hare a gangamin yakin neman zaben ‘yan siyasa a kasar, al’amarin da ke cusa shakku ga zabukan da za’a gudanar a watan Aprilu.Da dadewa ne dai hukumomin kula da tsaro a Nigeria ake zarginsu da rashin tabuka komi a yankin na Niger Delta mai arzikin man Petir a kasar, sai dai kuma Muhammadu Dikko yace zasu dauki matakai domin tabbatar da tsaro a lokutan zabe a yankin.  

Talla

kalaman Muhammad Dikko Abubakar akan tabbatar da tsaro a lokacin zabe

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.