UN

Majalisar Dunkin Duniya ta amince da bukatar daukar Mataki akan Cote d’Ivoire

Kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar Dunkin Duniya ya nada wani kwamitin binciken rikicin siyasar kasar Cote d’Ivoire bisa bukatar da kungiyar kasashen yammacin kasashen Africa ta gabatarwa Majalisar akan fargaba da keta hakkin bila dama da ake yi a kasar bayan kammala zaben shugaban kasa a watan Nuwamba.Kwamitin ya amince da bukatar Nigeria ne a madadin kasashen Africa wadanda suka amince da Alassane Ouattara a matsayin halattacen shugaban kasa tare da Allah waddai da ta’addanci da ya biyo bayan zaben da shugaban kasar Luarent Gbagbo yaki amincewa ya sauka bayan ya sha kaye.An dai daura wa kwamitin binciken alhakin gano masu hannu wajen haddasa rikicin kasar wanda majalisar Dunkin Duniya ta kiyasta mutuwar mutane sama da hamsin a rikicin.Rikicin dai ya biyo bayan kin amincewar Mista Gbagbo ya mika mulki ga abokin hamayyarsa Alassane Ouattara wanda duniya ta tabbatar da cewa shi ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Nuwamba. 

Gawar wani Mutum a Abidjan bayan gabza fada da jami'an tsaro
Gawar wani Mutum a Abidjan bayan gabza fada da jami'an tsaro Reuters/Luc Gnago
Talla

Kalaman Tsohon Shugaban Nigeria Gen. Gowon akan kiransa ga Laurent Gbagbo

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI