SUDAN

Rikici na neman haramta bukukuwan ‘yancin kudancin Sudan

Wata yarinya rike ta tutar yankin kudancin Sudan a daidai  lokacin da aka bayyana sakamakon zaben jin ra'ayin jama'ar yankin.
Wata yarinya rike ta tutar yankin kudancin Sudan a daidai lokacin da aka bayyana sakamakon zaben jin ra'ayin jama'ar yankin. Reuters/Tim McKulka/Unmis Handout

Tuni dai al’ummar yankin kudancin Sudan suka fara shirye shiryen gudanar da gagarumin bukin samun ‘yanci a Juba amma kuma rikici da ke yawan faruwa a kan iyakokin yankin arewaci da kudanci na neman kawo tarnaki ga shagulgulan samun ‘yancin kasar.Wani tsohon shugaban ‘yan tawayen yankin kudanci Wilson Achan ya bayyana cewa sun shirya gudanar da gagarumin buki inda zasu yi kade kade da raye raye don nuna murna.A watan Janairu ne aka gudanar da zaben jin ra’ayin jama’ar kudancin Sudan, inda kuma sama da kashi cas’in suka amince da ballewa daga Arewacin Sudan domin samun ‘yantartar kasa a watan Juli.A yanzu haka dai rikici ne ba kyaftawa ke ta abkuwa tsakanin ‘yan tawaye da sojojin wasu jahohi uku dake kudancin Sudan, rikicin da ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane.A lokacin yakin basasa a shekarar 1983 zuwa 2005 an kyasta cewa mutane miliyan biyu ne suka rasa rayukansu a kasar Sudan, al’amarin da ke cusa shakku ga rayukan al’amma a daidai lokacin da yankin kudanci ya karbi ‘yanci.A makon da ya gabata ne shugaban yankin Kudanci Salva Kirr ya yi wata ganawa ta gaggawa da takwaransa na yankin Arewaci Shugaba Umar Hassan Al Bashir domin tattauna yadda zasu shawo kan matsalar.