AU

Taron kungiyar tarayyar Africa kan rikicin kasar Libya

Taron kungiyar Tarayyar Africa a Addis Abba da aka gudanar a kwanukan baya.
Taron kungiyar Tarayyar Africa a Addis Abba da aka gudanar a kwanukan baya. REUTERS/Irada Humbatova

Wakilai da dama ne na shugaban kasar Libya Muammar Gaddafi suka halarci taron kungitar Tarayyar Kasashen Africa AU da ake gudanarwa yanzu haka a Birnin Addis Ababa don tattauna yadda zasu shawo kan rikicin kasar Libya. Taron dai ya hada da wakilan kungiyar Tarayyar Africa da wakilan Majalisar Dunkin Duniya da kuma na kungiyar kasashen Larabawa.Shugaban hukumar kungiyar ta AU Jean Ping ne ya mika sakon gayyatar ga Gaddafi, sai dai kuma wakilan bangaren ‘yan adawa da shugaban basu amsa gayyatar kungiyar ba.A jawabin Mista Ping lokacin fara taron yace ganawar da wakilan Gaddafi wata dama ce ta tattauna yadda za’a dauki mataki a halin da kasar Libya ta shiga tare da samar da hanyoyin magance rikicin.A safiyar yau ne dai Mista Ping ya dawo Birnin Addis Ababa daga kasashen Turai inda ya gana da Ministan harakokin wajen kasar Faransa Alain Juppe da Catherine Ashton ta kungiyar Tarayyar Turai.Mohammed al-Zwai na daya daga cikin wakilan Gaddafi daga kasar Libya tare da wasu Ministoci kasar guda hudu.Catherine Ashton, ta kungiyar Tarayyar Turai na daga cikin wadanda suka halarci taron da Nick Westcott, mai bada shawara ga kungiyar Tarayyar Turai kan lamurran da suka shafi Africa sai kuma wakilin Majalisar Dunkin Duniya Abdul Illah Alkhatib.