Nigeria

‘Yan adawa a Nigeria zasu kauracewa muhawarar ‘yan takara

Yantakarar neman kujerar shugabancin kasar Nigeria a jam’iyun siyasar CPC da ACN-da ANPP sun yi watsi da gayyatar halartar mahawara tsakanin yan takarar shugabancin kasar guda 4, da kafofin yada labaran gwamnatin kasar suka shirya. Bisa dalilin kauracewa muhwarar farko da shugaban kasar ya kauracewa da gidan Telebijin NN24 ya shirya a kasar. 

Dan takarar Neman kujerar Shugaban kasa karkashin Tutar  Jam'iyyar CPC Gen. Muhammadu Buhari
Dan takarar Neman kujerar Shugaban kasa karkashin Tutar Jam'iyyar CPC Gen. Muhammadu Buhari RFI Hausa
Talla

Kalaman Alhaji Ibrahim Modibbo Daraktan yada labaran kungiyar yakin neman zaben Nuhu Ribado wanda ya kare matakinsu

‘Yan takarar sun kafa hujjar cewa ba zasu halarci duk wata muhawara ba da shugaban wadanda kafofin yada labaran gwamnati zasu shirya domin shugaban da mataimakinsa sun kauracewa muhawarar da kafofin yada labaran kasar masu zaman kansu suka gudanar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI