Libya

Dakarun Kasashen Yammacin Duniya sun zafafa hare haren haramta shawagin jiragen sama a Libya

Reuters/ECPAD/Marine nationale/Cyril Davesne/Handout

Dakarun kasashen Yammacin Duniya sun yi barin wuta wa na Shugaban Libya Muammar Gaddafi a yankin gabashin kasar, abunda ya taimaka wa masu adawa su karfafa zaman su a garin Ajdabiyah.Kungiyar Kasashen Tarayyar Afrika, ta bayyana cewa tana shiga tsakanin neman kawo karshen rikicin, amma Kungiyar Tsaro ta NATO-OTAN ta ce zai aiki watanni uku tana aikin tabbatar da hana shawagin jiragen sama a sararin samaniyar kasar.Wani habsan sojan Amurka ya bayyana cewa Shugaban na Libya Gaddafi, wanda ya rasa ta cewa kan sararin samaniyar kasar, ya fara horas da sojojin haya, wadanda zasu yi masa yaki.