Cote d’Ivoire

Neman karfafa takunkumi wa Gbagbo na Cote d'Ivoire

Yan kasar Cote d’Ivoire da suka milyan guda sun tsere wa rikicin siyasar kasar, dake kara jefa kasar kusa da yakin basasa.Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD, ta ce cikin watanni hudu da suka gabata, mutane sun tsere wa rikicin siyasar kasar, inda Laurent Gbagbo ke ci gaba da karfa karfa kan madafun iko, duk da cewa Alassane Ouattara hukumar zabe ta aiyana a matsayin wanda ya lashen zaben.Yanzu haka an mika wa Kwamitin Sulhun MDD kudiri dake neman kara matsin lamba wa tukunkumi wa Laurent Gbagbo da ‘yan kazanginsa.Kudirin yana samun goyon bayan Faransa da Nigeria, kuma ana saran amincewa da shi nan bada jimawa ba. 

REUTERS/ Simon Akam