Libya

Dakarun Gaddafi na Libya sun ja da baya

REUTERS/Suhaib Salem

Zaratan jiragen saman yakin Faransa sun lalata jiragen saman Yakin Libya biyar da masu saukan ungulu biyu na dakarun dake biyayya wa shugaba Muammar Gaddafi.Wani kakakin gwamnatin Faransa, ya bayyana cewa sun cimma jiragen yayin da suke shirin tashin kai hari daga Misrata, abunda ya saba wa kudirin Kwamitin Sulhun MDD.Lamarin ya faru bayan masu adawa da gwamnatin kasar sun kwace garin Ajdabiyah daga hanun Gaddafi, bayan farmakin da kasashen duniya suka kaddamar na haramta shawagin jigaren sama.Rohotanni sun bayyna masu adawa da gwamnatin Gaddafi sun shiga Brega, tare da samun nasarar dannawa zuwa birnin Sirte.