Cote d’Ivoire

Ouattara na Cote d'Ivoire ya yi watsi da nadin mai shiga tsakani

REUTERS/Luc Gnago

Mutumin da kasashen duniya ke dauka a matsayin Shugaban kasar Cote d’Ivoire, Alassane Ouattara ya yi watsi da nada sabon mai shiga tsakani kan rikicin siyasar kasar da kungiyar kasashen Tarayyar Afrika ta yi.Ya zargi sabon mai shiga tsakanin Jose Brito tsahon Ministan Harkokin Wajen Cape Verde da cewa yana da halaka da Laurent Gbagbo, wanda ke ci gaba da karfa karfa kan madafun iko.Magoya bayan Gabgbo sun gudanar da gangami a birnin Abidjan, domin nuna goyon baya wa mutumin da duniya ta juya wa baya.Zaben kasar ta Cote d’Ivoire da MDD ta saka ido, ya tabbatar da nasara wa Alassane Ouattara, amma Gbagbo ya yi watsi da sakamakon.