Cote d’Ivoire
Dakarun Ouattara na ci gaba da kwace iko da kasar Cote d'Ivoire
Wallafawa ranar:
Dakarun dake biyayyawa zababben shugaban kasar Cote d'Ivoire ALssane Ouatara na ci gaba da kwace garuruwan kasar daga hanun Laurent Gbagbo.Rahotanni daga kasar Cote d’Ivoire, sun ce magoya bayan zababen Ouattara, dake dauke da makamai sun kutsa kai birnin San Pedro mai tshar jiragen ruwa tare da kwacewa daga masu goyon bayan Gbagbo, tunda fari magoya bayan na Ouattara sun kwace iko da garin Yamoussoukro, dake dauke da fadar Gwamnati kasar.Wannan daidai lokacin da MDD ta tsaurara takunkumin kan Gbagbo da 'yan kanzaginsa.