Cote d’Ivoire

Fada ya kai birnin Abidjan na kasar Cote d'Ivoire

Général Philippe Mangou, Babban habsan sojan Côte d’Ivoire da ya tsere
Général Philippe Mangou, Babban habsan sojan Côte d’Ivoire da ya tsere RFI/Norbert Navarro

Karar makamai ya barke a birnin Abidajn na kasar Cote d’Ivoire, inda ake kai ruwa rana tsakanin dakarun Alassane Ouattara dana Laurent Gbagbo.Wannan shi ne matakin karshe na neman kawar da Gbagbo daga madafun iko, bayan shan kayi yayin zaben watan Nowamban shekarar data gabata ta 2010.Tuni Babban habson sojan Cote d’Ivoire na bangaren Gbagbo, Janar Phillippe Mangou ya nemi mafaka shi da iyalansa a ofishin jakadancin kasar Afrika ta KuduYanzu haka fadan ya kai barikin sojan dake kusa da fadar Laurent Gbagbo, inda ofisoshin jakadanci suke.Alassane Ouattara da duniya ke dauka zababben shugaban kasa, ya nemi sauran sojan kasar su bashi goyon baya, ya kuma tabbatar da cewa mayakan dake masa biyayya sun shiga birnin Abidjan, kuma nan bada jimawa zasu kwace birnin daga Gbagbo, wanda shi ne birni na karshe mai mahimmaci da ya rage a hanun dakarun Gbagbo.