Cote d’Ivoire

Mayakan dake biyayya wa Ouattara na Cote d’Ivoire sun kwace iko da garin San Pedro

AFP photo/Zoom Dossp

Mayakan dake biyayya wa Alassane Ouattara da duniya ke dauka zababben Shugaban kasar Cote d’Ivoire yau Alhamis sun kwace iko da garin San Pedro mai tashar jiragen ruwa.Garin ya na da mahimmanci wajen fitar da coco da kasar ke kaiwa kasashen duniya.Da sanyan safiya magoya bayan Ouattara suka karbe ikon da garin, inda yanzu haka suke ci gaba da sintirin tabbatar da doka da oda, kamar yadda mazauna birin suka tabbatar wa manema labarai.Magoya bayan Ouattara sun baiwa Laurent Gbagbo dake ci gaba da karfa karfa kan madafun ikon kasar wa’adi ya sauka daga mulki kafin su isa birnin Abidjan, mafi mahimmci da ya rage a hanun masu yiwa Gbagbo biyayya.Dakatun masu biyayya wa Ouattara sun ce birnin Abidjan shi ne wanda suke hako na gaba, domin raba Gbagbo da abun da ya rage a hanunsa na madafun iko.MDD ya kara kaimin takunkumin da aka zarga wa Gbagbo da ‘yan kanzaginsa.