Tunisiya

Shugaban Hukumar zaben Tunisiya ya yi barazanar ajiye aiki

PM kasar Tunisiya Béji Caïd Essebsi
PM kasar Tunisiya Béji Caïd Essebsi AFP/FETHI BELAID

Shugaban Hukumar zaben kasar Tunisia, Yad Ben Achour, ya yi barazanar aje aikin sa, saboda korafin da jami’ansa suka yi, kan nada Habib Essid, wani na kusa da Tsohon shugaban kasa, Zine el Abidine Ben Ali, a matsayin Minista.Achour ya zargi wasu daga cikin jami’an nasa, da yunkurin zagon kasa. Kasar ta Tunisiya dake yankin Arewacin Afrika ta neman farfadowa daga juyin juya halin da ya yi awun gaba da tsohon shugaba Ben Ali, bayan mulkin shekaru 23. Kuma guguwar wannan sauyi ci gaba da kadawa cikin sauran kasashen Larabawa.