Cote d’Ivoire

Har yanzu babu cikaken tsaro da zaman lahiya a garin Abidjan na kasar Cote-D’Ivoire

Yanayin da al'umma su ke ciki a garin Abidjan na Cote-D'Ivoire
Yanayin da al'umma su ke ciki a garin Abidjan na Cote-D'Ivoire

Kwana guda da kama Laurent Gbagbo,garin Abidjan babban birnin kassuwanci da tattalin arzikin kasar ta Cote-D’Ivoire ya kassance har yanzu babu cikeken tsaro.A yayin da wasu ke murna, wasu na kukawa tare da tada hankalin jama’a . A na jin karen bindigogi kadan-kadan a cikin wasu unguwani na masu goyon bayan tsohon shugaban kasar.Maganar zaman lahiya da girka gwabantin hadin kan yan kasa ita kowa ke gani babban ginshikin kawo gina kasar Cote-D’Ivoire sabuwa bayan wanan dogon rikici.