Libya

An Kaddamar da sabbin matakan aiki da kudirin MDD kan kasar Libya

Kungiyar Tsaro ta NATO ko OTAN ta zafafa hare hare kan Tripoli babban birnin kasar Libya, inda aka ji kararraki masu yawa. Ana kai farmakin da zumma tabbatar da aiki da kudirin MDD da ya haramta shawagin jiragen sama a sararin samaniyar kasa, da kuma kare fararen hula.Gwamnatin kasar ta bayyana cewa mutane uku sun hallaka sakamakon hare haren.Wani babban jami’in gwamnatin kasar ta Libya ya bayyana cewa shugaban kabilun garin Misrata sun yi alkawarin kawar da ‘yan tawayen idan dakarun gwamnati ba suyi haka ba.