Burkina Faso

Dage dokar fitar dare a birnin Ouagadougoun Burkina Faso

Ouagadougou
Ouagadougou © Ahmed Ouoba

Gwamnatin kasar BF ta dage dokar hana fitar daren da ta saka tun ranar 16 ga watan Aprilun da ya gabata sakamakon boren da sojoji suka tayar a garin wagadagu babban birnin kasar, kamar yadda ma’aikatar ministan tsaron kasar ta sanar a jiya.Dokar hana fitar da aka kafa daga 7 na yamma zuwa 6 na safe a birnin wagadugu ta samo asali ne sanadiyar boren da wasu sojoji suka tayar ne, wadanda suka fantsama a cikin gari suna farfasa shagunan jama’a domin nuna cewa basu ji dadi ba daga irin yadda gwamnatin kasar bata kyautata masu.