Uganda

Shugaban Museveni Uganda ya fatattaki masu zanga zanga

Reuters

Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya facaccaki masu zanga zangar nuna adawa da gwamnatin kasar kan tashin farashin kayayyaki abinci da man fetur.Ya kuma zargi jami’an ‘yan sanda da alkalai da nuna tasauyawa wa mutanen da yak ira barayi. Shugaba Musevini ya kuma zargi kafofin yada labarai na ciki dana waje da daure gindi wa masu zanga zangar.Yan sandan kasar ta Uganda sun cafke madugun ‘yan adwan kasar Kizza Basigye sau hudu, wanda ya sha kayi yayin zaben watan Febrairu. Kuma nasarar da shugaba Museveni ya samu ta harzika ‘yan adawa.