Najeriya

Sojojin Nigeria sun hallaka wasu 'yan sanda a garin Lagos

Sojojin Nigeria sun kashe wasu 'yan Sanda hudu, cikinsu harda shugaban tashar 'yan Sandan Badagry, DPO Samuel Salihu, a wani harin ramako, saboda harbe wani Staff Sergeant har lahira da wani Dan Sanda ya yi a karshen mako.Rohotanni sun ce, Dan Sandan ya harbe sojin ne yayin da yake cikin farin kaya, abinda ya harzuka sojin daukar fansa.Kakakin rundunar 'yan Sandan Nigeria, Olusola Amore, ya ce Rundunar zata gudanar da bincike dan hukunta wadanda suka aikata aika aikan.