An fara shirin yadda za a tafiyar da kasar Libya, bayan shugaba Ghaddafi

Shugaban Libya Muammar Ghaddafi
Chanzawa ranar: 09/06/2011 - 12:05

kungiyar Kawancen Tsaro ta NATO, ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta fara shirin yadda za’a kula da kasar Libya, bayan kauda shugaba Muammar Ghaddafi.Bayan taro kan halin da ake ciki, kungiyar ta kuma amince da kara wa’adin kai hare hare na watanni uku, kamar yadda Sakataren ta, Anders Fogh Rasmussen ya bayyana.Ya celokaci yayi, da za’ayi shiri kan bayan rikicin da ake, batun da ake yanzu, ba wai lokacin da Ghadafi zai tafi bane, domin lalle zai tafi, saboda haka ya dace kasashen duniya su shirya matakin da zasu dauka, domin NATO ba zata cigaba da zama a Libya ba.