Masu rajin kare demokaradiya sun yi watsi da sauye sauyen Morocco
Wallafawa ranar:
Masu raji neman girka demokaradiya na kasar Morocco, sun bayyana cewa sauye sauye da Sarki Mohammaed na VI, ya kawo basu isa ba.Sun bayyana shirin gudanar da zanag zanga ranar Lahadi, domin neman tabbatar da karin sauye sauye na siyasa.Sauye sauye da Sarkin kasar ta Morocco Mohammed na VI na ya maince da su, sun hada da kara karfi wa mukamun PM, wanda za a zaba daga jam’iyyar mai rinaye cikin majalisar dokoki, da amince da harshen kabilun ‘yan tsiraru na Berber.Amma Sarkin zai ci gaba da rike iko da mahimma kafofi da suka hada da rindunar soja. Jiya Jumma’a Sarkin kasar ta Morocco ya bayyana sauye sauye cikin jawabi ga al’umar kasar.