Libya

'Yan tawayen Libya sun ce babu yiwuwar Ci Gaba da zaman Kadhafi a kasar

Reuters/Zohra Bensemra

Yayin da kotun hukunta manya laifufuka ta majalisar dinkin duniya ta bayar da sammacin cafke shugaban kasar Libya Muammar Kadhafi, Shugaban ’yan tawayen kasar, Mustafa Mohammed Abdel Jalil, yace yazu babu yuwuwar a bar shugaba Kadhfi ya ci gaba da zama a kasar. Shugaban ‘yan tawayen yace an bukaci su bar Khadhafi ya ci gaba da zama a kasar, amma hakan ya saba wa doka, don haka a cewa shi, ba makawa sai Kadhafi ya fuskanci hukunci.