Libya

Magoya bayan Shugaban Libya Gaddafi zasu ci gaba da fada

AFP/EURONEWS

Magoya bayan Shugaban kasar Libya Muammar Gaddafi sun aniyar ci gaba da fada, ko bayan kungiyar tsaro ta NATO-OTAN, ta kawo karshen hare haren da take kaiwa.Yan tawaye da kasashen Yammacin Duniya na ci gaba da matsa lamba wa gwamnatin Gaddafi kan ta yi murabus.Dan shugaban Saif al-Islam, ya shaida wa tashar talabijin ta kasar cewa bayan sadaukar da kai da suka yi, babu maganar komawa da baya, Kuma ko NATO tan ako bata nan, sai sun samu nasarar yakin da aka fara.