Somaliya

Sabon Fada ya barke cikin kasar Somaliya

Reuters

Rahotanni Daga Mogadishu babban birnin kasar Somaliya, na nuna cewar, an samu barkewar fada, sakamakon bude wutar dakarun Gwamnati, dake samun goyan bayan dakarun kungiyar kasahsen Tarayyar Afrika ta AU.Jami’in dake kula da agaji, Ali Muse, ya ce an samu barkewar fadan a sassa daban daban na birnin, amma ya zuwa yanzu babu adadin wadanda suka jikkata.Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da Hukumar Samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta fara jigilar abinci zuwa kasar.