Cote d’Ivoire

Shugaban Cote d'Ivoire ya yi godiya wa Nigeria

Shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara
Shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara

Shugaban Kasar Cote D’Ivoire, Alassane Ouattara, ya yaba da rawar da Nigeria ta taka wajen warware rikicin siyasar kasar sa, a ziyarar sa ta biyu da ya kai kasar, bayan karbar ragamar mulki.Cikin watan Afrilu Ouattara ya karbi madafun ikon kasar ta Cote d'Ivoire daga Laurent Gbagbo wanda yaki amincewa da shan kayi, bayan zaben watan Nowamba na shekara ta 2010. Kasasehn duniya suka taimaka Ouattara ya karbi ikon tafiyar da kasar.