Nijar

An tarwatsa masu zanga zanga kan Rashin Hasken wutar lantarki a Janhuriyar Niger

CIA

Jami’an tsaron kasar Janhuriyar Niger sun tarwatse daruruwan masu zanga zanga kan rashin hasken wutar lantarki, tare da cafke wasu daga ciki.Yan sandan sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen kan masu zanga zangar na garin Tanout, kamar yadda wani gidan rediyon kasar ya bayyana.Wani jami’in ‘yan sanda ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa cewa masu zanga zangar sun lalata ofishin hukumar samar da hasken wutar lantarki. Akwai mutane 20 da suka jikata sakamakon faruwan lamarin.