Nigeria-Britain-Italy

Birtaniya na Binciken Bidiyo mutanen da aka yi garkuwa da su a Nigeria

Taswirar Nigeria mai dauke da manuniyar Jahar Kebbi a arewacin kasar
Taswirar Nigeria mai dauke da manuniyar Jahar Kebbi a arewacin kasar

Hukumomin Birtaniya sun ce suna gudanar da wani binciken hoton Bidiyo wanda ke dauke da hotunan wasu turawan ingila da italiya da aka yi garguwa dasu a Nigeria a watan Mayu.Kamfanin Dillacin Labaran kasar Faransa AFP wanda ya samu Hoton Bidiyon a ofishinsa dake Abidjan Babban birnin kasar Cote d’Ivoire, bidoyon ya nuna hoton turawan a murkushe da gwiwowinsu tare da wasu ‘yan bindiga su uku a tsaye sanye da rawani.A yanzu haka dai gwamnatin Birtaniya tace tana kan tattaunawa da hukokomin Nigeria da Italiya tare da kamfanonin da turawan ke aiki a Nigeria.Turawan, ma’aikatan wani kamfanin kasar Italiya B. stabilini a Nigeria, kuma an yi garkuwa da su ne bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai masu farmaki a Birnin Kebbi a arewacin Nigeria.Sai dai kuma ana zargin cewa wadanda suka yi garkuwa da turawan ‘yan kungiyar Al Qaeda ne.