Somaliya

Kasar Somalia ce kan gaba ga aikin ta’addanci

'yan fashin jirgin ruwan Somalia
'yan fashin jirgin ruwan Somalia AFP / MOHAMED DAHIR

Wani Bincike da aka gudanar ya nuna cewar, kasar Somalia ce kasa ta farko da aka fi samun ayyukan ta’adanci a duniya, yayin da Pakistan, Iraq, Afghanistan, da kuma Sudan ta kudu ke bi mata bi da bi.Binciken da wani kanfani mai suna Maplecroft ya gudanar, yace ana fuskantar barazanar aiyukan ta’adanci a kasashen Yemen, Iran, Uganda, Libya, Masar da kuma Nigeria.