Nigeria

Kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun bukaci cafke Modo Sheriff

Kofar Shiga Birnin Maiduguri Jahar Borno a Tarayyar Najeriya.
Kofar Shiga Birnin Maiduguri Jahar Borno a Tarayyar Najeriya. RFI Hausa

Daya daga cikin masu rajin kare Hakkin Bil Adama a Nigeria, Barr. Femi Falana, ya bukaci hukumomin Nigeria, da su kama Tsohon Gwamnan Barno, Madu Shariff, dangane da zargin alakar sa da kungiyar Boko Haram.A wata kasida da ya gabatar a Jami’ar Lagos, lauyan yayi zargin cewar, Tsohon Gwamna yayi amfani da kungiyar Boko Haram wajen cim ma bukatunsa. 

Talla

Kalaman Femi Falana

“ina kira don kama Tsohon Gwamnan Barno, Madu Shariff, da kuma gurfanar da shi a gaban kotu, saboda rawar da ya taka, wajen anfani da kungiyar Boko Haram, da kuma kashe shugaban ta, Muhammad Yusuf, matakin ya biyo bayan yadda Tsohon Gwamnan da takwaransda na Bauchi suka nemi gafara kungiyar, ya dace su yiwa ‘yan Nigeria bayani akai”.

Sai dai kuma a nasa bangaren tsohon Gwamnan Jahar Borno Alh. Modu sheriff yace

Tsohon Gwamnan Borno Alh. Modu sheriff

Femi Falana bai san halin da suke ciki ba a Jahar Maiduguri da manufofin gwamnati akan kungiyar Boko Haram ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.