UN-NIGERIA

UN zata gabatarwa Jonathan rehoton kwararar Man fetir a Niger Delta

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Hukumar kula da muhalli ta Majalisar Dunkin Duniya UNEP zata gabatarwa shugaban Nigeria Goodluck Jonathan wani rehoton kwararar man Fetir da aka kwashe tsawon shekaru 50 yana tsiyaya a yankin Niger Delta.Hukumar ta UNEP tace wannan rehoton shi ne irinsa na farko da ya shafi yankin Niger Delta wanda kuma ake sa ran zai taimakawa gwamnatin kasar wajen magance matsalar.A jiya laraba ne dai kamfanin hakar man Fetir na Shell ya bayyana daukar alhakin gurbatar yanayi a yankin na Niger Delta tare da biyan diyya ga al’ummar da al’amarin ya shafa da suka rasa matsiguninsu.Tun a shekarar 1950 ne kamfanin Shell ke hako man Fetir a Nigeria, sai a shekarar 1993 ne kamfanin ya dakatar da aiki a a kasar. Sai dai kuma har yanzu akwai sauran kayayyakin kamfanin a yankin Ogoni a yankin Nigeri Delta.