Somaliya

Gwamnatin Somali ta karbi ikon Mogadishu

Dakarun kungiyar Al Shabab lokacin da suke ficewa daga birnin Mogadishu
Dakarun kungiyar Al Shabab lokacin da suke ficewa daga birnin Mogadishu

Gomnatin Somali ta bada sanarwar karbe ikon birnin Mogadishu bayan samun galabar ‘yan tawayen kungiyar Al Shabab, dake kokarin kifar da gwamnatin kasar.Sanarwar dai ta fito ne daga fadar shugaban kasar Somaliya Sheikh Sharif Ahmed, bayan da kungiyar Al shabab ta fara janye dakarunta.Sai dai kuma, kakakin kungiyar ta Al shabab Sheikh Ali Mohamud ya musanta ikirarin na gwamnatin kasar, al’amarin da yace sun fara janye dakarunsu ne domin sake wani sabon salon dabarun yaki.