Somaliya

Gwamnatin Somaliya ta yi tayin Afuwa ga Al Shabab

Taswirar kasar Somaliya
Taswirar kasar Somaliya RFI

Gwamnatin Somaliya ta yi tayin Afuwa ga ‘yan Tawayen kungiyar Al shababa dake adawa da gwamnatin kasar bayan janye dakaru da kungiyar ta yi daga Mogadishu babban birnin kasar.An dai dade ana gwabza yaki da kungiyar Al Shabab, tun a shekarar 2007 da suka nemi kifar da gwamnatin kasar dake da goyon bayan kasashen yammaci.A cewar kakakin gwamnatin kasar ta Somaliya, Abdulrahman Osman, sun yi tayin Afuwa ga Al Shabab idan har suka aje makamai suka hada hannu wajen cid a kasa gaba.