Nijar

An kammala shirye shiryen aikin Hajji a Nijar

Tutar Kasar Jamhuriyar  Nijar
Tutar Kasar Jamhuriyar Nijar RFI Hausa

Ministan Harakokin cikin gidan Jamhuriyar Nijar, Audu Labbo, yace sun kammala karbar kudaden maniyatan aikin hajjin bana, ranar biyar ga wata, saboda haka wadanda basu samu daman biyan kudadensu kafin wannan lokaci ba, su yi hakuri.A cewar Ministan, Hajji kiran Allah ne wadanda basu samu zuwa ba ya zama dole su yi hakuri har zuwa lokacin da Allah ya karbi kiransu domin a yanzu an kammala duk wani shirye shirye na zuwa aikin Hajji. 

Talla

Kalaman Audu Labbo Ministan harakokin cikin gidan Nijar

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.