UN-Africa

Magance matsalar Abinci a Africa na bukatar $103, inji UN

halin Matsanancin yunwa da karancin Abinci da ake fama da shi a kasar Somalia
halin Matsanancin yunwa da karancin Abinci da ake fama da shi a kasar Somalia ®Reuters

Hukumar kula da Abinci ta Majalisar Dunkin Duniya tace matsalar yunwa da karancin abinci na bukatar kudi Dala 103 cikin gaggawa domin bunkasa aikin noma tare da yaki da matsalar karancin abinci a kasashen Africa.A rehoton na majalisar Dunkin duniya kimanin mutane sama da Miliyan 3 ke cikin matsanancin halin yunwa a kasar Somaliya, mutane Miliyan 12 kuma ke cikin halin matsanancin karancin abinci a kasashen Africa musamman Ethiopia da kasar Kenya.Hukumar kula da abinci ta Majalisar Dunkin Duniya tace tana neman kudi Dala Miliyan 161 domin kare rayukan mutane a Africa, kodayake a yanzu haka hukumar tace ta samu tallafin kudi kimanin Dala Miliyan 57. A daya bangaren kuma, kasar Amurka tace zata taimaka da tallafin kudi dala Miliyan 105 ga kasashen da ke fama da yunwa a kasashen Africa.