Niger-Nigeria

Ziyarar shugaban Jamhuriyyar Niger a Najeriya

Shugaban Jamhuriyyar Nijar Mahamadou Issoufou,
Shugaban Jamhuriyyar Nijar Mahamadou Issoufou, ©RFI/Delphine Michaud

A ziyarar aiki da shugaban Jamhuriyar Niger, Muhammadu Yusuf, ya kai a Najeriya, shugaban ya gana da shugaba Goodluck Jonathan, da kuma al’ummar Niger da ke zaune a Najeriya.A lokacin da yake ganawa da ‘yan Nijar, shugaban yace jinjinawa Najeriya a irin rawar da take takawa wajen ganin ci gaban Jamhuriyyar Nijar. 

Talla

Kalaman Shugaban Jamhuriyyar Nijar Muhammadu Yusuf

A cewarsa, akwai dankon zumunci tsakanin Najeriya da Nijar, domin a bangaren siyasa Najeriya na daya daga cikin kasashen da suke taimakawa Jamhuriyyar Nijar.

Shugaban kuma ya nemi ‘yan Nijar da su kasance masu bin doka da Oda a Najeriya dama sauran kasashen duniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.