Cote d’ivoire

Mutane 26 suka mutu a Cote d’Ivoire watan jiya, inji UN

Dakarun kasar Cote-D'Ivoire
Dakarun kasar Cote-D'Ivoire Reuters/Luc Gnago

Majalisar Dunkin Duniya tace kimanin mutane 26 aka kashe watan jiya a kasar Cote d’Voire, kuma ‘yan kasar suna zargin dakarun da ke goyon bayan shugaban kasar Alassane Ouattara da aikata kisan wanda aka rantsar a watan Mayu.Wani wakilin hukumar kare hakkin bi’adama ta Majalisar Dunkin Duniya Guillaume Ngefa yace kashe kashen sun auku ne a sassan yankunan kasar kuma sun shafi magoya Laurent Gbagbo.Sai dai kuma ya bayyana cewa magoya bayan Gbagbo sun kai wani hari hari a yammacin kasar inda suka kasha mutae da dama. A wasu yankunan kuma Majalisar Dunkin Duniya ta bada rehoton barkewar rikici tsakanin dakarun Alassane Ouattara da wasu matasa inda aka samu rasa rayuka.Rashin mika mulki ga Allassane Outtara da Gbagbo ya yi bayan ya sha kaye a zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Nuwamban bara shi ya jefa kasar cikin rikici inda dubun dubatar ‘yan kasar suka rasa rayukansu.