Libya

Gaddafi ya yi watsi da jita-jitar zai gudu daga Libya

Shugaban kasar Libya Muammar Gaddafi
Shugaban kasar Libya Muammar Gaddafi © REUTERS

Shugaban Kasar Libya, Muammar Ghaddafi, ya yi watsi da rade-radin da ‘Yan Tawaye da Kungiyar NATO ke yi, na cewa yana shirin barin kasar, yayin da ‘Yan Tawayen ke kara matsawa zuwa birnin Tripoli.Wata sanarwa da shugaban ya bayar, da aka yada ta kafofin yada labarai, shugaban ya yi alkawarin murkushe ‘Yan Tawayen da ya kira beraye, da kuma Yan mulkin mallaka, inda yake cewa, ya kusan samun nasara.Shugaban ya bukaci magoya bayan sa, da su tirjewa ‘Yan Tawayen da kungiyar NATO, su kuma dauki damarar yaki domin kare kasarsu.