Somaliya

An zargi ‘yan Tawayen Somaliya da cin zarafin Bil’adama

halin Matsanancin yunwa da karancin Abinci da ake fama da shi a kasar Somalia
halin Matsanancin yunwa da karancin Abinci da ake fama da shi a kasar Somalia REUTERS/Feisal Omar

Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Human Rights Watch, ta zargi ‘yan tawayen somaliya, da cin zarafin Bil Adama a wani rehoto da kungiyar ta wallafa.Rehoton kungiyar ya zargi kungiyar Al Shabaab da kashe fararen hula, baji ba gani, yayin da aka kuma zargi dakarun Gwamnati da kamawa da kuma tsare mutanen da basu aikata laifi ba.Rahoton ya bukaci bangarorin biyu, da su tsagaita wuta a tsakaninsu, don barin fararen hula su samu agajin abinci, yayin da kuma aka zargi kasashen Yammacin duniya da rashin daukar matakan da suka dace don kawo karshen cin zarafin.Mawallafin rahoton, Ben Rawlence, yace kungiyar Al Shabaab na cin zarafin Jama’ar da ke yankin da take rike da shi a kowace rana, saboda haka ya dace ta dauki alhakin duk wani cin zarafin da aka samu a Yankin, da kuma yadda ta ke kai harin kan mai uwa da wabi.Rahotan ya kara da cewa, yayin da ita ma gwamnati ke kame mutane tana tsarewa, ba tare da bincike ba, wadanda suka gudu zuwa kasar Kenya, na fuskantar matsalolin da suka hada da fyade, kwace musu dukiya daga hannun ‘Yan Sandan Kenya.