Masar

Alkalan kasar Masar sun kawo karshen nuna shari'ar da ake wa Mubarak

tsohon shugaban Misra Hosni Mubarak
tsohon shugaban Misra Hosni Mubarak REUTERS/Egypt TV via Reuters

Alkalin kasar Masar ya bayyana kawo karshen nuna shariyar tsohon Shugaban kasar Hosni Mubarak da aka yi kai tsaye ta kafofin yada labarai, abunda ya harzika masu zanga zanga.An saka ranar biyar ga watan gobe na Satumba domin ci gaba da saurarn karar, inda ake tuhumar tsohon Shugaba Mubarak da wasu makaranba da ‘ya’yansa biyu da laifukan daban daban da suka hada da bada umurnin hallaka masu zanga zanga, kafin kawo karshensa gwamnatinsa.