Malawi

Mutane 19 sun hallaka a zanga zangar kasar malawi

Reuters/Eldson Chagara

Mutane 19 suka hallaka, yayin da wasu kimanin 60 suka samu raunika, lokacin zanga zangar nuna kiyayya wa gwamnatin Shugaba Bingu wa Mutharika ta kasar Malawi.Kamar yadda rohoton kungiyar kare hakkin bil Adama ta gwamnatin kasar ya bayyana, kuma wannan ya zama alkaluma na farko da mahukunta suka fitar tun bayan hargitsin na watan jiya na Yuli.Ana saran masu zanga zangar kasar ta Malawi zasu ci gaba cikin wannan mako, domin nuna rashin jin dadi kan tsadar rayuwa.