Angola

An sami Rashin fahimtar juna a majalisar kasar Angola

Yan adawa na jam’iyyar UNITA, sun fice daga cikin majalisar dokokin kasar Angola, bayan zargin jam’iyyar MPLA mai mulki da neman gurgunta aiyukan kwamitin zabe na kasar.Wannan yayin da ake shirin tunkarar babban zaben kasar cikin shekara mai zuwa. Cikin shekara ta 2002, aka kawo karshen yakin basasan kasar ta mai arzikin man fetur.